Ga araha ga amfani: Fa'idoji 6 dake
tattare da cin dabino

Dabino yana daya daga cikin 'ya'yan itatuwa
masu matukar amfani ga jikin adam saboda
irin sinadaren da ya dauke dashi. Dabino
yana girme ne a bishiya kuma 'ya'yan na
cure ne kuma ya fi son yanayi mai zafi.
Bayan 'ya'yan dabinon sun nuna ana iya
cinsu hakan nan kokuma a cire kwallon
da ke ciki a sarrafa su ta wasu hanyoyin
don more lagwada da amfanin da
dabinon ke dauke dashi.
Ga dai wasu fa'idoji guda shida da
dabino keyi a jikin dan adam.
Wasu fa'idoji bakwai da dabino ke yi ga jikin dan-
adam
1) Dabino nada tasiri wajen kara kuzari ga
masu aure
Binciken masana kimiyyan sinadaren
abinci ya nuna cewa dabino yana da
matukar muhimmanci wajen kara kuzari
tsakanin ma'aurata.
Domin samun wannan fa'idar, sai mutum
ya debi dabino kamar cikin hannunsa ya
jika su cikin nonon akuya su kwana, da
safiya sai a marka dabinon tare da nonon
kuma ana iya kara zuma da cardamom.
Wannan hadin yana da mutukar amfani
wajen inganta kwanciyar aure.
2) Maganin gudawa
Dabino da ya nuna sosai yana dauke da
sinadarin potassium wanda ke da
mutukar muhimmanci wajen magance
gudawa.
Sinadarin fibre da ke cikin dabino kuma
yana taimakawa wajen magance basir da
sauran matsalolin da ke da alaka da fitar
bayan gida da gyaran ciki.
3) Lafiyar zuciya
Dabino yana da matukar amfani wajen
karawa wa zuciyar dan adam lafiya. An fi
samun fa'idan da ke cikin dabinon idan
an tsoma shi cikin ruwa ya kwana sai a
dauko a ci da safe. Hakan yana da
matukar amfani ga masu fama da ciwon
zuciya.
Sinadarin Potassium da ke cikin dabinon
yana kare buguwar zuciya da wasu
cututuka masu kama da hakan.
4) Karin kuzari
Dabino na dauke da suga wanda basu da
ila ga jikin dan adam kamar glucose,
fructose da sucrose. Saboda hakan duk
lokacin da mutum ke jin kasala idan yaci
dabino zai samu kuzari nan take.
5) Karfafa garkuwan jiki da magance allergy
Wani abin mamaki game da dabino shine
yadda take dauke da sinadarin sulphur
wanda ba'a cika samunsa a 'ya'yan
itatuwa ba amma kuma yana da matukar
amfani da jikin dan adam cikinsu kuwa
harda kara karfin garkuwar jiki da
magance
6) Yana taimakawa masu son mayar da
jikinsu
Dabino na dauke da suga, sinadarin
Protein da ke gina jiki da kuma vitamins.
Kilogram daya da dabino na dauke da
calories 3,000 wanda hakan sun isa jikin
dan-adam biyan bukatun ta na kwana
daya.
Idan mutum ya rame kuma yana son
mayar da kibansa, dabino na iya
taimakawa wajen gina jiki sai mutum ya
jibinci cin dabinon.