Dandalin Kannywood: Soyayyar
Rahma Sadau da Messi da kuma
Neymar

- Fitacciyar 'yar finafin Hausa ta Kannywood
Rahma Sadau ita masoyiyar 'yan wasan
kwallon kafa ce
- Hakan ya bayyana ne a shafinta na
dandalin sada zumunta da muhawara na
Instagram a inda ta lika hotunan Messi da
Neymar fitattun 'yan kungiyar Barcelona
Dandalin Kannywood: Soyayyar Rahma Sadau da
Messi da kuma Neymar
Daga dukkan alamu da akwai wata
soyayya mai karfi tsakanin fitacciyar 'yar
finafinan Hausa ta Kannywood Rahma
Sadau da taurarin kwallon kafa Messi da
kuma Neymar na kungiyar Barcelona.
Hakan ya bayyana ne a shafinta na
dandalin sada zumunta da muhawara na
Instagram a inda ta lika hotunan Messi
da Neymar fitattun 'yan kungiyar
Barcelona a lokacin da suke murnar cin
kwallo.
Messi da Neymar na kungiyar Barcelona
Sai dai a sakon na ta, jarumar ba ta
banbance barcin makaho ba, ma'ana, ko
soyayyarta ga kungiyar kwallon kafan ce
ko kuma ta fitattun 'yan wasan ne biyu.
A karawar da aka yi ta baya-bayan nan
kungiyar Barcelona ta lallasa ta PSG da ci
6 da 1 a camp Nou, bayan ta sha kashi da
ci 4 da nema a karawar farko.
Rahama Sadau ba ita kadai ce ba a cikin
'yan finafinan Hausa da suke marawa
kungiyar Barcelona baya tare da nuna
matukar sha'awarsu ga taurarin kwallon
kafa ba.
Jarumi kuma matashi Muhammad Bello
Muhammad da aka fi sani General PMB
na garin Jos, saboda kaunarsa ga
kungiyar Barcelona har rana aka ware a
bikinsa a inda aka yi shiga ta musamman
ta kungiyar.