Dandalin Kannywood: Jaruma
Ai'sha Tsamiya ta sharara karya a
bainar jama'a

A cikin wani lamari mai matukar kunya da
dariya, an bankado jirgin fitacciyar jarumar
nan ta fina-finan Kannywood mai suna
Ai'sha Aliyu da aka fi sani da Tsamiya inda
aka gano cewar jarumar ta sharara karya ne
kawai a bainar jama'a a cikin wani shiri na
gidan Talabijin na Arewa24.
Mun samu dai cewa a kwanan baya ne
jarumar ta sanar da samun gurbin
karatun ta a budaddiyar jami'ar nan ta
gwamnatin tarayya da ake yiwa lakabi da
National Open University (NOUN) a
turance domin ta yi karatun kimiyyar
lafiya watau Health Technology.
Dandalin Kannywood: Jaruma Ai'sha Tsamiya ta
sharara karya a bainar jama'a

Essmah.cf amma ta samu daga majiyar mu
cewa ba a yin wannan kwas din a jami'ar
kamar dai yadda Daraktan Watsa Labarai
na jami'ar, Malam Ibrahim Sheme, ya
fada wa majiyar ta mu.
Da yake karin haske, jami'in yada labarai
na jami'ar ya kuma bayyana cewa
watakila dai jarumar na so ne ta cewa
Public Health don kuwa shine kadai kwas
din da jami'ar ke koyarwa da ya danganci
lafiya.
Daga nan ne kuma sai ya jinjinawa
jarumar game da yadda take da zummar
yin karatu ba kamar sauran wasu matan
ba.