Dandalin Kannywood: Ban mutu ba
ina nan da raina - Sani Moda

- A yayin zantawar da manema labarai
suka yi da shahararren jarumin finafinan
Hausan nan Idris Sani Moda ta waya, ya
karyarta jita-jitar da ake ta yadawa a
kafafen yada labarai na zamani cewar ya
rasu a daren jiya Litinin
Dandalin Kannywood: Ban mutu ba ina nan da raina
- Sani Moda
A yayin zantawar da manema labarai
suka yi da shahararren jarumin finafinan
Hausan nan Idris Sani Moda ta waya, ya
karyarta jita-jitar da ake ta yadawa a
kafafen yada labarai na zamani cewar ya
rasu a daren jiya Litinin.

Sani Moda ya kara da cewa ya yi
mamakin yadda labarin mutuwar tasa ta
yadu, wanda a dalilin hakan yake ta
faman shan kira daga ciki da wajen kasar
nan daga wurin masoyan sa, domin
tabbatar da gaskiyar al'amarin. A cewar
shi, an sami kuskuren sanarwar ne daga
asibitin da yake kwance, inda suka
bayyana shine a matsayin wanda ya rasu,
ya bayyana cewar bashi Allah ya amshi
rayuwar tasa ba na kusa dashi ne ya
amsa kiran Allah. Sannan kuma ya
bayyana cewar yana cigaba da samun
lafiya.
A jiya ne dai kafafen yada labarai suka
dinga yada cewar Allah yayi wa fitaccen
jarumin rasuwa, bayan ya jima yana
fama da jinya. Muna masa adu'ar Allah
ya bashi lafiya mai inganchi yasa kuma
hakan ya zama kaffara ce a gare shi.