Dandalin Kannywood: Auren 'yan
fim 6 ya mutu a wannan shekarar

Rahotannin da muke samu daga majiyar mu
ta Fim mai wallafa mujallar da ta shafi
harkokin fina-finan Hausau ta bayyana cewa
kimanin akalla auren mata 'yan fim shidda
ne ya mutu a shekarar nan da muke ciki ta
2017.
Haka ma dai mujallar ta bayyana hakan
tamkar wani babban bala'i ko kuma
annoba da ta fadawa 'yan masana'antar
kasantuwar ba'a taba samun mace-
macen aure da yawan da suka kai haka
ba a cikin shekara daya.
Dandalin Kannywood: Auren 'yan fim 6 ya mutu a
wannan shekarar
KU KARANTA: Ronaldo ne yafi kowa iya
kwallo a duniya
Essmah dai har ila yau ya samu cewa
ganin haka ne ma ya sanya majiyar tamu
ta shiga yin bincike don sanin ainahin
musabbabin mutuwar auren na jaruman
masana'antar.
Wasu daga cikin matan dai sun bayyana
cewa laifin mazan ne domin kuwa sun sa
yaudara wajen neman auren nasu yayin
da wasu kuma daga cikin matan suka
bayyana cewa mazajen nasu ba su basu
abinci.
Da majiyar tamu ta tuntubi wasu mazan
da lamarin ya shafa daya daga cikin su ya
bayyana cewa ita wadda ya auran tace
wai bata son kishiya ne shi kuma ya ga
kamata su rabu da ita.
Matan dai da auren nasu ya mutun sun
hada da Fauziyya Maikyau, Maryam Isah,
Fati Al-Amin, Aisha Tafida, Safiya Kishiya
da kuma Asma'u Musa.