Dalilin mu na kin goyawa Buhari
baya - Kungiyar dattijan Arewa

Kungiyar dattijan Arewa (ACF) ta bayyana
dalilin ta na kin bayyana goyon bayan ta ga
takarar shugaba Buhari a zaben 219.
ACF ta ce 'yan Najeriya masu katin kada
kuri'a ne kawai zasu raba gardamar
waye zai zama shugaban kasar Najeriya a
219.
Sakataren kungiyar, Dakta Anthony Sani,
ya soki shugaba Buhari bisa yin shiru da
ya yi a kan kashe-kashen dake faruwa a
wasu sassan Najeriya.
Yayin ziyarar da shugabancin ACF ya kaiwa Buhari
Da yake magana a kan dalilin da yasa
ACF bata bayyana goyon bayan ta ga
takarar Buhari, Sani ya ce, "kungiyar ACF
uwa ce ga kungiyoyin dake magana da
yawun mutanen arewa.

Sannan ya cigaba da cewa, " ba hurumin
ACF bane ta zabawa jama'a dan takarar
da zasu zaba ba saboda ba kungiyar
siyasa ba ce."
Kazalika ya ce bashi da tabbacin ko
kungiyar ACF ta gamsu da kokarin
shugaba Buhari a kan karagar mulki.