Buhari ya dakatar da babbar
kwangilar da Amaechi ya kawo
Yahudawan Israila suyi ta biliyoyin
kudi

- A farkon makon nan ne, shugaban kasa
Muhammadu Buhari ya tsayar da sabuwar
kwangilar tsaro da 'yan majalisar zababbun
shi na gwamnatin tarayya suka kirkiro
domin zargin zamba
- Kwangilar da kwamitin zababbu na
Gwamnatin tarayya ta sa hannu a watan
Disamba 2017, zata ci dala miliyan 195 inda
zata samar da jirage na musamman ga
sojojin sama na Najeriya
Buhari ya dakatar da babbar kwangilar da Amaechi
ya kawo Yahudawan Israila suyi ta biliyoyin kudi
Daga baya, The Guardian ta ruwaito cewa
kwangilar zata tabbatar da samar da
helicopter 3, aircraft 3, jiragen yaki na
ruwa 3, da kuma nau'ikan ababen
sufurin ruwa 12, sai motoci masu aiki a
ruwa da tudu don tsare hanyoyin ruwa
na Najeriya.
Ministan sufuri na Najeriya, Rotimi
Amaechi shi ya kawo kwangilar. An
kalubalanci kwangilar da cewa da cewa
wannan kawai hanya ce da ministan ya
kirkiro don sata.
A wata takarda da shugaban sojojin sojoji
ya aikawa shugaban kasa, Abba Kyari, ya
umarci Antoni janar na Najeriya,
Abubakar Malami da ya dakatar da
kwangilar, shugaban kasar ya kuma
umarci mai bada shawara akan harkokin
tsaro da kuma hukumar leken asiri da ta
binciki yanda wadanda aka ba kwangilar
a tabbatar sun mallaki 'security
clearance' na aikin ba tare da shaidar
karshe ba.

umarta da asa 'yan kwangilar dasu
samarda kayayyaki na kimanin dala
miliyan 50 wanda suka fara karba.
'Yan kwangilar HSLi, wanda ministan
yace kamfanin Isra'ila ne, bashi da
shaidar kasuwanci ta Isra'ila, wani
binciken Premium Times ya nuna.
Suna da dangantaka ne da Mitrelli, wani
kamfanin Isra'ila wanda yake da
dangantaka da ministan.