Boko Haram za su mika wuya -
Aisha Wakil

Lauya mai kare hakin bil-adama da kuma
yin sulhu, Hajiya Aisha Wakil wanda akafi
sani da Mama Boko Haram tace a kwana-a-
tashi mayakan kungiyar Boko Haram za su
mika wuya kuma su koma gidanjensu.
A jawabin ta yi wajen taron neman
taimako na gidauniyarta, a ranar Asabar
a garin Maiduguri, Wakil ta ce 'yan Boko
Haram din suna ta niyyar ajiye
makamansu inda suka ce suna son su
dawo gida wajen iyalensu.
Boko Haram za su miya wuya - Aisha Wakil

"Dukkan yara na da ke cikin daji za su
fito kuma su mika wuya saboda a samu
zaman lafiya ," inji ta.
Mama Boko Haram tayi alkawarin cigaba
da gwagwarmaya don ganin an samu
zaman lafiya mai dorewa na jihohin da
ake samun tashin hankula.
"Ba zan yi kasa a gwiwa ba wajen tin
sulhu har sai na tabbatar an sako duk
wadanda suke hannun 'yan Boko Haram ."
A yayin da take tsokaci kan ayyukan
gidauniyar ta mai suna 'Complete Care
and Aid', ta ce an kafa gidauniyar ne
saboda bayar da kulawa ga wadanda
masifar ta'addancin ya shafa wanda suka
hada da marayu da wandanda suka rasa
muhallinsu.
Wakil ta ce gidauniyar za ta bayar da
gudunmawa a bangarorin ilimi, kiwon
lafiya da taimakawa wadanda rikicin ya
shafa ta hanyar shawarwari da tallafi.