Barcelona za ta karbi bakuncin Real Madrid a
gasar La liga a karawar hamayya ta Clasico karo
na 238 a ranar Lahadi.

Karawar na zuwa a yayin da Barcelona ke cikin
shaukin bikin lashe kofin La liga da Copa del Ray,
yayin da Real Madrid kuma ke murnar kai wa wasan
karshe a gasar zakarun Turai karo na uku a jere.
Real Madrid ta ce ba za ta karrama Barcelona ba a
matsayinta na wadda ta lashe kofin La liga kafin
fara fafatawar.
Barcelona ta taba karrama Real Madrid a 2008
bayan ta lashe kofin La liga.
Amma Zinedine Zidane ya bayyana rashin jin dadi
kan yadda Barcelona ta ki karrama 'yan wasansa
bayan sun lashe kofin duniya na kungiyoyin kwallo
kafa.
Wasu na ganin karawar ta ranar Lahadi ba ta da
wani muhimmaci, saboda tuni Barcelona ta karbi
kofin La liga, kamar yadda Real Madrid ta mayar da
hankali ga karawarta da Liverpool a gasar zakarun
Turai
Sai dai kuma wasanni hudu suka rage Barcelona ta
kammala kaka ba tare da an doke ta ba a La Liga.
Barcelona ta buga wasa 41 ba a doke ta ba a
La Liga
Zakarun Turai: Yadda Real Madrid ta doke
Bayern Munich
Bayan lashe kofin La liga karo na bakwai a shekaru
10 a ranar Lahadin da ta gabata, yanzu abin da
Barcelona ta sa a gaba shi ne kammala La Liga ba
tare da an doke ta ba.
Barcelona za ta so ta kafa wannan tarihin a gasar
La liga a Spain, yayin da kuma Real Madrid za ta
nemi hana wa Barcelona kafa tarihin.
A nata bangaren kuma Real Madrid da ke matsayi
na uku a tebur, za ta nemi karbe matsayi na biyu ne
a hannun Atletico Madrid.
Don haka wasan Clasico a ranar Lahadi zai yi zafi
kamar yadda aka saba gani.
Tazarar maki 15 Barcelona ta ba Real Madrid kuma
za ta so ta kara yawan makin zuwa 18, wanda zai
kasance tazara mafi girma da Barcelona ta ba Real
Madrid a tarihin hamayyarsu.
Sannan Zidane zai yi kokarin rama kashin da ya sha
ci 3-0 a Santiago Bernabeu a hannun Barcelona a
watan Disemba.
A ranar 26 ga Mayu ne Real Madrid za ta fafata da
Liverpool a wasan karshe a gasar zakarun Turai a
birnin Kiev na Ukraine.
Madrid na harin lashe kofin gasar ne karo na 13.
Kaftin din Madrid, Sergio Ramos ya ce idan suka
lashe kofin gasar zakarun Turai zai shafe nasarar da
Barcelona ta samu na lashe kofuna biyu a Spain.
Sannan ya ce za su bi umurnin kocinsu na kin
karrama Barcelona a ranar Lahadi.
A tarihin Clasico, Real Madrid ta samu nasara a
karo 95 yayin da Barcelona ta samu nasara karo
93.
Idan har Real ta ci kwallo daya zai kasance kwallo
ta 400 da ta ci Barcelona a tarihin Clasico.
Barcelona kuma ta ci Real Madrid kwallaye 387.
Wannan haduwar za ta kasance ta 38 ga Andres
Iniesta kuma Clasico ta karshe ga Kaftin din na
Barcelona kafin ya bar kulub din a karshen kaka.