Babu masaka tsinke: An yi taron
murnar kara tsayawar Buhari takara
a jihar Jigawa

- Magoya bayan jam´iyar APC a jihar Jigawa
sun gudanar da taron gangamin nuna goyon
bayan shugaba Buhari da gwamna Badaru
Abubakar
- An gudanar da taron a filin kwallo na
karamar hukumar Gumel kuma ya samu
halattar kusan duk wani mai ruwa da tsaki
dake jam´iyar APC a jihar
- Wani matashin dan siyasa, Mahadi Aminu
Taura, ya ce shugaba Buhari da gwamna
Badaru tamkar sun ci zaben 2019 sun gama
Magoya bayan jam´iyar APC a jihar
Jigawa sun gudanar da taron gangami
domin nuna goyon bayansu ga shugaban
kasa Muhammadu Buhari da Maigirma
Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji
Muhammad Badaru Abubakar a zaben
shekarar 2019 mai zuwa.
An yi taron murnar kara tsayawar Buhari takara a
jihar Jigawa
An yi taron murnar kara tsayawar Buhari takara a
jihar Jigawa
Taron wanda akayi a filin kwallo na
karamar hukumar Gumel ya samu
halattar kusan duk wani mai ruwa da
tsaki dake jam´iyar APC tare da sauran
mambobin ta a jihar.
DUBA WANNAN: Mawakin da ya yi wakar
cin zarafin Allah da manzon sa a Kano ya
shiga hannu
Wasu daga cikin masu ruwa da tsaki sun
hada da Alhaji Isa Muhammad Gerawa
wanda ya kasance shine shugaban
kwamitin gudanar da taron, tsohon
senator mai wakiltar jigawa ta gabas
maso yamma, Sanata Danladi Sankara, da
sanatan yankin mai ci a yanzu, da
shugaban jam´iyyar Alhaji Ado Sani Kiri,
'yan majalisar tarayya da na jiha, da yan
majalisar zartarwa na jiha, da kuma
shugabannin kananan hukumomi da
sauransu.
An yi taron murnar kara tsayawar Buhari takara a
jihar Jigawa
An yi taron murnar kara tsayawar Buhari takara a
jihar Jigawa
Wani matashin dan siyasa, Mahadi
Aminu Taura, da ya halarci taron, ya
shaidawa wakilin naij.con cewar,
shugaba Buhari da gwamna Badaru
tamkar sun ci zaben 2019 sun gama
saboda irin kwazon da kishin son
cigaban kasa da al'umma da suka nuna.
An yi taron murnar kara tsayawar Buhari takara a
jihar Jigawa
An yi taron murnar kara tsayawar Buhari takara a
jihar Jigawa