Babban magana: Wata matashiya
ta garzaya wata kotun Najeriya don
neman izinin auren mace 'yar
uwarta

- Wasu iyaye a Najeriya sunyi hannun riga
na har abada da diyarsu bayan sun gano
tana son ta auri wata 'yar uwarta mace
- Matshiyar da iyayenta suka sallamata ta
garzaya wata kotu inda ta bukaci a daura
mata aure da wata 'yar uwarta mace
- Kotun ta ki amincewa da wannan bukatar
kuma iyayenta sun sanar a jarida cewa sun
sallamata har abada
Duk da cewa dokokin Najeriya sun
haramta aure tsakanin jinsi iri daya,
masoya da dama na jinsi iri daya sukan
fito fili su bayyana wa jama'a cewa suna
soyaya sai dai ba kasafai ake samun
wanda suka tunkarar kotu don daura
musu aure ba.
Wata matashiya mai suna Shalom
Shoremi yar asalin jihar Ogun ta hadu da
fushin iyayenta inda har suka sallamata
ga duniya bayan sun gano ta tafi wata
kotun tarayya inda ta bukaci a daura
mata aure da wata macen.

Iyayenta da sauran 'yan uwanta sunyi tir
da abinda ta aikata har ma sun sanar da
cewa sun sallamata har abada a shafukan
jaridu na kasa.
Wata matashiya ta shigar da kara wata kotun
Najeriya saboda an hana ta auren 'yar uwarta mace
Kamar yadda sanarwar jaridar ta
bayyana, kotun ta ki amincewa da
bukatar matashiyar saboda ya ci karo da
dokar hana auren jinsi guda na 2014,
wanda ya yi bayani karara cewa laifi ne
yin auren jinsi a dokar Najeriya.
Dokar kuma ta akwai hukuncin zaman
gidan kaso na shekaru 14 ga wadanda
aka samu suna soyaya tsakanin jinsi iri
daya.
Bayan bayyana cewa sun sallamata ga
duniya, iyayen Shallom sun kara da cewa
sun haramta mata cin gadonsu har
abada.
A wata labarin, 24blog.com.ngta ruwaito cewa
Prime Ministan kasar Ingila, Theresa May
ta yi kira ga Najeriya ta janye dokar hana
auren jinsi guda. Ta kuma mika irin
wannan rokon ga sauran kasashen da
Ingila ta raina.