Asirin wani kwarto da ya je yin
fyade ga tsohuwa mai shekaru 110
ya tonu

- Kwamacala kenan, jami'an tsaro sunyi ram
da wani kasurgumin kwarto
- Kuma yanzu haka yana can gida Maza
garkame, bayanda aka damke shi
Kotu ta ingiza keyar wani kwarto dan
shekara 56 gidan kurkuku bayan da yan
sanda suka gurfanar da shi bisa zargin
nufin haikewa wata tsohuwa mai shekaru
110.
Asirin wani kwarto da ya je yin fyade ga tsohuwa
mai shekaru 110 ya tonu
Dan sanda mai gabatar da kara sufeto
Insp. Caleb Leranmo, ya shaidawa kotun
cewa, sun kama mutumin ne ranar 30 ga
watan Afrilu, yayin da ya afka gidan
gyatumar dake gida mai lamba 12 a layin
Igbehin a garin Ado Ekiti. A cewarsa,
wannan laifi ne da ya saba da sashi na
359 na kudin manyan laifuka (2012) na
jihar ta Ekiti.

Bayan sauraron karar ne, mai shari'a
Taiwo Ajibade, ya bayar da umarnin
tafiya da shi gidan yari kafin ranar 22 ga
watan Mayu domin cigaba da shari'ar.