2019: Ba na tunanin za a gudanar
da zabe, Najeriya za ta tarwatse
kafin lokacin - Adeboye

A ranar Juma'ar da ta gabata ne babban
limamin cocin Redeemed Christian, Fasto
Enoch Adeboye, ya gargadi gwamnatin kasar
nan da cewar ta yi gaggawar kawo karshen
kashe-kashe a sassa daban-daban na kasar
nan.
Babban Limamin ya yi gargadin cewa
muddin aka ci gaba da zuba idanu kan
halin da kasar nan take ciki na zubar da
jini dan Adam ba tare da hakki ba to
kuwa za a wayi gari ba bu ballantana
labarin ta.
Fasto Adeboye ya yi wannan gargadi a
yayin gudanar da harkokin su na ibada
inda yake cewa muddin ba a kawo
karshen kashe-kashe ba to ko shakka ba
bu lallai zaben 2019 ya tabbata a kasar
nan ta Najeriya.
Fasto Adeboye da Shugaba Buhari
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa,
babban limamin ya bayyana irin halin
damuwa da suka shiga da iyalin sa a
kasar Jamus yayin da suka samu rahoton
makiyaya da suka kai hari wani coci a
karamar hukumar Gwer ta jihar Benuwe.

A yayin haka kuma babban limamin ya
jagoranci mabiyansa wajen gudanar da
addu'o'i da zasu warware matsalolin da
kasar nan ke fama, inda ya ce duk da
kasancewa kasar nan ta farfado bayan
yakin basasa ba bu yadda za a yi hakan
ya maimaitu muddin rikicin addini ya
keto.
A sanandiya Fasto Adeboye ya ke mika
kokon barar sa ga shugaban kasa
Muhammadu Buhari akan ya tashi tsaye
wajen kawo karshen wannan rikici kafin
ya sauya fasali zuwa na addini.