Tusa a jirgin sama aba ce da ke damun mutane. Me yake jawo yawan tusar a jirgi? Ta yaya za mu yi maganin wannan abin kunya? David Robson ya tattauna da wani likita dan Denmark wanda ke da amsoshi na ban mamaki.
Sha'awar Jacob Rosenberg ta sanin yadda lamarin tusa a jirgin sama ta ke yawan damun mutane ta soma ne a lokacin da ya yi wata doguwar tafiya a jirgin zuwa New Zealand.
Ya duba cikinsa ne sai ya lura cewa ya kumbura tun lokacin da ya shiga jirgin. Lokacin da ya bude jakarsa ya dauko robar ruwansa sai ya ga ba ruwa sai ya fara fahimtar abin da ya faru.
Ya fahimci cewa lokacin da yake cikin jirgin saboda yanayin iskar da ke cikin jirgin robar ta kumbura, da jirgin ya sauka ta motse.
Rosenberg ya kwatanta iskar da ke cikinsa da abin da ya faru da wannan robar ruwa tasa.
''Tun daga wannan lokacin ne na fara lura da yawan tusar da mutum ke yi lokacin da ya hau jirgin sama, wadda tana da yawa sosai.'' In ji shi.
Duk da cewa ba za ka iya hada iskar waje da ta cikin jirgi ba wajen baci, amma duk da haka mutane na korafi sosai da warin iskar cikin jirgin sama domin tana damun yawancin mutane.
''Idan ka yi wa mutane magana a kai, za ka ji kowa ya gaya maka cewa ya taba jin warin tusa a wani lokaci,'' In ji Rosenberg wanda farfesa ne a Jami'ar Copenhagen.
To amma masanin bai tashi tunanin illar lamarin ba ta fannin kimiyya sai a lokacin da ya sauka daga jirgin, suna shan lemo da abokanan aikinsa daga nan ne ya fara tunani sosai a kan hakan.
Sakamakon abin da ya biyo baya ita ce wata takarda da za ta iya rage mana wannan abin damuwa da ke takura mana a jirgi.
Ko a kasa ma ba a jirgi ba dukkan mu mukan yi tusa, mu fitar da iska mai yawan gaske da za mu yi mamaki.
Kamar yadda wani kiyasi ya nuna yawancin mutane mukan yi tusa sau goma a cikin sa'oi 24, inda muke fitar da kusan lita (liter) daya gaba daya.
Iskar da muke fitarwa (tusa) tana samuwa ne daga abincin da muke ci wanda bai narke, ya bi jikinmu ba,inda kwayoyin bakteriya (bacteria) suke rubar da abincin, daga nan sai ya samar da iskar nitrogen da carbon dioxide(iska mai dumi da muke fitarwa daga hancinmu ta numfashi) da hydrogen da sauran sinadaran sulphur( dangin farar wuta) masu wari.
Wannan abu ne da zai iya kasancewa a ko ina ana fama da shi, amma lokacin da Rosenberg, ya bincika littattafan kimiyya, sai ya gano cewa akwai abubuwa da yawa da aka yi musu bahuguwar fahimta a kan tusar da muke yi.
Duk da yadda mutane da yawa suka dauka, bincike ya nuna cewa maza ba su kai mata yawan yin tusa ba.
Kuma wannan nazari da aka yi a wuraren shekarun 1990 ya nuna cewa tusar mata ta fi ta maza wari, saboda yawan sinadaran farar wuta wadanda ke da wari a cikin ta matan.
Duk da yadda aka dauki wake a matsayin abincin da ke sa tusa (musical fruit), wani gwaji da aka yi kwanannan an gano cewa bai kai yadda yawanci mutane suke dauka ba wajen sa tusa, kuma tasirinsa ya dogara ne daga yanayin kowana mutum.
Kayan abincin da ke rage yawan tusa sun hada da kifi da shinkafa da kayan madara da ruwan lemo(juice), saboda sauransu ba sa raguwa a cikin mutum ta yadda za su rube.
Idan a kullum kana tusarka a kasa ba tare da kowa ma ya sani ba, ko kuma ba a damuwa da ita, a jirgin sama lamarin ba haka yake ba, domin aba ce mai damun mutane.
Yawan tusa a jirgi in ji Rosenberg kimiyya ce mai sauki, kamar yadda ya bayyana.
Idan jirgi ya tashi sama,'' karfin iskar da ke dannowa kasa daga sama (pressure ) zai ragu, saboda haka ita kuma iskar da ke wuri sai ta fadada ta cika sauran wurare.''( wato ke nan
wadda take cikin mutum sai ta buda ta cika wa mutum ciki, inda ciki kuma ke rage ta ta hanyar tusa).
Idan ba a manta ba, a can baya mun ce mutum yana fitar da akalla lita daya ta iska (tusa) a sa'a 24.
To wannan lita daya, idan ka tashi a jirgi tana bukatar mazubi wato cikinka ke nan a nan ya kara girma da kashi 30 cikin dari, kafin ya iya daukarta, abin da ke sa cikinka ke nan ya kunbura.
Wannan matsala ce da yawancin masu tukin jirgin sama ke fama da ita, inda sama da kashi 60 cikin dari ke kukan yawan kumburin ciki fiye da galibin masu aikin ofis.
Za ka iya kokarin rike tusarka ba shakka, to amma hakan ba dabara ba ce, in ji Rosenberg; bayan takura da za ka yi, shi yana ganin akwai dan hadari.
Ya ce, ''idan kai matashi ne kuma kana da lafiya, rike tusar ba matsala ba ce, amma a wurin tsoho, hakan zai iya sa ta takura aikin zuciyarsa.''
Sakin tusar ma a cikin jirgi yana da irin hadarinsa kamar yadda wani bincike da ke wata makala da aka gabatar a 1969, ya nuna cewa, wuta za ta iya tashi daga tusar 'yan
sama jannati idan tusar ta yi tsanani a cikin jirginsu.
To sai dai kawo yanzu ba a taba samun wannan hadari ba. Kuma duk da haka ma wasu masana na hukumar ayyukan sama jannati ta kasar Canada, sun bayar da shawarar amfani da
kayan abincin da ya kunshi waken soya da aka riga aka ruba shi (wanda ba zai sake ruba ba a ciki), da cewa su ne suka fi dacewa a jirgin sama jannati.
Saboda su wadannan daman suna dauke da kwayoyin bakteriya da za su yi gogayya da kwayoyin bakteriyar da ke haifar da iska, wanda hakan zai rage kumburin cikin da 'yan sama jannatin kan yi fama da shi.
Anfani da kamfai mai burbushin gawayi;
Duk da haka Rosenberg yana ganin akwai yadda ya fi dacewa a bullo wa matsalar.
Yana ganin za a iya amfani da gawayi a kujerun jirgi ( idan aka sarrafa gawayi yana hana bazuwar wari).
Ko da ike dai gwajin da aka yi a baya ya nuna cewa hakan ba ya tasiri sosai saboda tusar tana biyowa ta cikin wandon mutum ne ko fatarin mace ta watsu, saboda haka gawayin da aka
hada a kujerar jirgin ba zai iya hana tusar wucewa ba.
A kan hakan Rosenberg yake ganin kamfanonin jiragen saman za su iya samun barguna da aka sarrafa aka sanya musu gawayin a cikinsu da mutane za su iya amfani da su.
Ko kuma idan mutum ya damu sosai da warin tusar tasa sai ya samu kamfai na musamman da ake sanyawa gawayin, hakan zai iya hana warin tusar fita idan ya yi.
Mujallar kimiyya ta abubuwan da suka shafi iska da ruwan cikin mutum ta Amurka ( American Journal of Gastroenterology) ta ruwaito cewa kamfai na musamman da aka saka masa gawayi a ciki yana dauke kusan kashi dari bisa dari na wari idan aka kwatanta da kunzugun gawayi na musamman da ake sanyawa a cikin wando wanda yake hana warin kashi 70 cikin dari.
Rosenberg yana kuma da wasu shawarwarin hanyar maganin wannan matsala ta tusa a jirgin sama, amma fa wadanda ba lalle su samu karbuwa ba.
Masanin yana ganin wasu mutanen masu tusar za su iya fitar da wata iskar ta rubabben abincin ta makogwaronsu, ta biyo ta baki, wanda yana ganin domin maganin hakan sai kamfanonin
jiragen sama su samar da wata na'ura ta musamman ta duba iskar da mutum yake fitarwa ta baki saboda irin abincin da ya ci.
Idan aka samu fasinja yana da matsala sai a sa shi a wani bangare na musamman na jirgin, kusa da bandaki ko kuma ya ce kawai a hana shi shiga jirgin ma.
Ganin yadda tusa a cikin jirgi take damun mutane abu ne mai muhimmancin gaske mu yi kokarin samo mafita a kanta, abin da ba mu dauka da muhimmanci ba.
Ko kuma mu ce watakila abin da ya fi kawai shi ne mu rika sakin tusarmu a duk lokacin da ta zo mana. Kamar yadda Rosenberg ya ce, ''tusa ba wata matsala ba ce ta daban, amma kuma
muna kawar da kanmu a kanta ba ma yin magana a kanta.''
Mu yi fatan bincikensa ya samu karbuwa a wurin masu iya maganin lamarin.
Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan How to tackle the most embarrassing problem on planes