Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci taron majalisar zantarwan jam’iyyar APC da daren yau Litinin, 26 ga watan Maris, 2018.
Shugaban kasan ya karbi bakuncin dukkan masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC a fadar shugaban kasa na Aso Rock da ke babbab birnin tarayya Abuja.
Daga cikin wadanda suka halarci taron sune mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo; shugaban majalisan dattawa, Bukola Saraki; shugaban jam’iyyar APC, John Oyegun; ministan birnin tarayya, Muhammadu Bello.
Shugaba Buhari ya jagoranci taron majalisar zantarwan APC
Sauran sune gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’I; gwamnan jihar Adamawa, Jibrilla Bindow; gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun; gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu; gwamnan jihar Jigawa, Mohammad Badaru; da gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.