Wani mataimakin sufurtandan da hukumar Kastan ya kashe kansa a kauyen Lungu, Gwarinpa, Abuja. har yanzu dai ba’a san dalilin da ya sabbaba hakan ba.Majiya ta bayyana cewa mutumin mai suna, Christian ya kulle kansa cikin dakine kuma ya rataye kansa da igiya ranan asabar.
Majiyar ta kara da cewa mutumin gwauro ne wanda ke zaune da dan uwansa kafin akayi mayar da dan uwan nasa jihar Legas.
Shugaban hukumar yan sanda Gwrainpa, CSP Nuruddeen Sabo, yace dan uwansa ya tafi aske gashi ne lokacin da abun ya faru.
“Da aka kai asibitin Kubwa, an tabbatar da cewa ya mutu. Abubuwan da aka samu ya kunshi wuka, da wasu kwayoyi.”