Yan Najeriya sun yi raddi ga addu’ar Fani Kayode ga Buhari
Femi Fani Kayode yayi mummunar fata ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ‘yan Najeriya da dama sun mayar masa da raddi daidai kalamansa Tsohon daraktan watsa labarai na yakin neman zaben tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan Fani Kayode yayi ma shugaban kasa Muhammadu Buhari mummunar fata yayin daya tafi birnin Landan don duba lafiyarsa


Fani Kayode ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook, inda yace: ‘An hana yan jaridu shiga fadar shugaban kasa, Shugaban kasa ya gana da yan matan Chibok a boye, Yanzu kuma an fitar da shi Landan don duba lafiyarsa, abin kamar fim.”
Fani Kayode ya cigaba da fadin: “Ina fatan shugaban kasa ya dawo lafiya, duk da cewa dai ina shakkar hakan, ina fatan Osinbajo ya cigaba da rike mulki na tsawon lokaci, daga bisani a rantsar da shi shugaban kasa mai cikakken iko.”
Yan Najeriya sun yi raddi ga addu’ar Fani Kayode ga Buhari Fani Kayode Dandalin Mujallrmu.com ta ruwaito a daren Lahadi 7 ga watan Mayu ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zarce kasar Ingila don duba lafiyarsa, hakan ya baiwa mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbako damar darewa karagar mulki.
Sai dai yan Najeriya da dama sun mayar masa da martani tare da yi masa kakkausar suka.
Wani mai suna Sulaiman yace “Sai dai idan babanka ne dan wiwi zai dawo ya cigaba da mulkkin rikon kwarya.”
Gabriel Opoola cewa yayi “Karya Fani Kayode keyi dayace wai ba’a bar yan jaridu shiga ba, bayan ga shi mun ga hotunan su.”
sai wani Abdulmalik yace “Ka cigaba da kalaman banza, zafin kayi da kuka sha ne bai sake ka ba.”