A Najeriya, jam'iyyar PDP ta ce babban burin ta shi ne ta sake fafata wa da shugaba Muhammadu Buhari a zaben shekarar 2019.
Jam'iyyar ta PDP bangaren Sanata Ahmed Makarfi, ta ce bata goyon bayan kiraye-kirayen da wasu 'yan kasar ke yi na neman shugaban ya yi murabus domin ya fuskanci jiyyar rashin lafiyar sa.
Sanata Ahmed Makarfi, ya shaida wa BBC cewa, PDP ba ta maraba da yin murabus din shugaba Buhari domin ta fi son idan lokacin zaben 2019 ya zo a nuna 'yar kashi.
A cewar sa, jam'iyyar PDP na sahun gaba wajen ba wa shugaba Muhammadu Buhari shawarar ya sake koma wa Ingila domin duba lafiyarsa, kuma matakin daya dauka yanzu ya nuna cewa shugaban ya yi amfani da wannan shawara.
Shugaban jam'iyyar ya kuma ce suna yi wa shugaba Buhari fatan samun lafiya, inda ya zargi gwamnatin APC mai mulki da boye gaskiyar halin rashin lafiyar shugaban kasar tun da farko.
Sanata Ahmed Makarfi, ya ce jinkirin da aka rika yi na komawar shugaba Buhari asibiti ka iya janyo tabarbarewar rashin lafiyar shugaban kasar