Ko Kana Daya Daga Cikin Wadanda Insunsa Kudi Da Daddare Su Tashi Da Safe Su Tarar AnKwasarmusu Kudi, Ko Sunma Kudin Gi'bi ??
Kana Daya Daga Cikin Wadanda Suke Samun SaKonni Akan An Cirar Musu
#100 Ko #50 Ko #25 Koma Naira #5 ??
Nasan Wasu Ma Sunata Kokari Domin Wajen Sunga Sunsamo Maganin Wadannan Matsalolin,
Wasu Kuma Da Dama Sun CanJa SIM Dinsu DuK Akan Kwasar Kudin Da Ake Musu
Wasu Kuma Kullun Aikinsu Kenan Suna Kirar Customer Care Domin Shigar Da KoraFe-KoraFen Su, Sai Kaga Sunce Sun CiremaKa DuK TsaruKan Da Ake Kwasarma Kudi .. Bayan KwanaKi Kadan Sai Kaga Abubuwa Sun Dawo Da Kwasar Ma KudinKa ...
Sai Dai Ku Sani, Idan 'Bera Nada Sata Toh Daddawama Nada Wari,
Abun Da NaKe Nufi Anan Shine, Wani Lokaci GasKiya Mu Da Kanmu Ke Jama Kanmu, Wani LoKaci MuKe Shiga TsaruKa Masu Cinye Mana Kudi ...
Ka Taba Ganin Message Kamar HaKa A WayarKa ??

A Duk Lokacin Da Ka Sami Irin Ko Makamancin Wannan Message Din Da Zarar Ka Taba "OK" Shikenan Saboda Idan Kun Lura Talla Ne Suke Maka Na Caller Tunes Ne Akan #50 , Amma InKa Taba "Cancel" Shikenan Ka Huta,
Wani Lokaci Kuma Zakaga Mutum Yayi Subscribtion Na FaceBooK, Ko WhatsApp, Amma Kuma Bayan Ka Cinye Subscribtion Din Bayan Wata Ya Kare Sai Kaga Sun Kuma Sun Cirarma KudinKa Ba Tare Da IzininKa Ba,
YANDA ZAKA FITA DAGA TSARUKAN CIKIN SAUKI
Da FarKo Idan Kwata - Kwata BaKaso Su Dinga Turama Message Din Da Zaisa Su Dunga Zararma Kudi Saika Danna *123*5*4# Idan Ka Danna Zasu Nunama , Options Kamar HaKa
1. Opt Out Mobile Ad
2. BacK,
Saika Shiga Option Na FarKo, Daganan Zasu Nuna Maka
" You Currently Receive Advitising Reply Yes To Option Out Op Advitising"
Saika Shiga Ka Rubuta YES Ka Tura, Shikenan Ka Fita Daga Tsarin Da Zasu Dinga Turama ire Iren Message Din Da ZaiDunga Ja Suna Zararma KudinKa
Na Biyu Kuma Idan Kanaso Kaga Tare Da Fita Duk TsaruKan Dake Sa Ana Cirarma KudinKa Saika Danna *123*5*1*2# Zai Nunama Options Guda Biyu
1, Available Content Service
2, My Active Services
SaiKa Zabi Option 2, Anan Ne ZaKaga Duk TsaruKan Da Suke Cinma Kudi, Anan Ne ZaKa Bi Kata Canceling Dinsu, A HanKali,
DuK Wanda Kakeson Cancel Sai Kahau Kansa, Ka Zabi Unsubscribe,
SHIKENAN!

Ku kasance da www.Arewafresh.cf akoda yaushe